Page 1
“Fatu! Fatu!! Fatu!!!” Inna dake zaune saman ta barma ne take kwalawa Fatu kira.
fitowa tayi daga ɗakin ta ƙarasa gaban ta tace “gani Inna”. Kallonta Inna tayi daga sama har kasa tace “haba Fatu yanzu ina zakije ki kayi wanan shegen adon nan naki irin na Aljanu?”
Turo baki gaba tayi tace “kin san fa yau ake Aure gidan mai gari kuma chan zani, nasan yanzu su Saude ma suna jirana kinsan fa mune k’irjin biki, Ni kuma Inna ki daina haɗa ni da Aljanu, duk garin nan banfi kowa iya kwalliya ba”
Sakin baki Inna tayi tana kallonta kafin tace “to kuwa ba in da zaki, ina ke ina zuwa gidan biki bikin ma na gidan mai gari in ba shashanci ba, yarinya dake”
ai kan ta barmar Fatu ta kwanta ta fara birgima da kuke kuke tana cewa “wlh sai naje Inna duk abinda za kiyi, kina son kar naci shinkafar gidan bikin ne ?” su Saude suyi ta min dariya Allah wlh nidai ki barni na tafi” ta fad’a tare da kara birgimar tana kuka kamar wanda aka duka, Inna tace “kaji min ja irar yarinya da iskanci nan kamar taɓa cin shinkafar ba ne?” Yarinya sai shegen gantalewar tsiya ba abinda kika iya sai yawo shiga nan fita nan duk mutanan garin nan ba wanda bai kawo min karan kina..,”
Kukan da takeyi ne ya tsaya cak cike da masifa tace “wani dan kutumar uban ne ya kawo kara na?” Wlh koshi wayen sai yaci gidan su kuwa a garin nan”
kallonta tayi tace “ki fara cin gidan mu kafin kici nasu fita ne dai ba zaki ba, Fashewa ta karayi da kuka tana cewa “don girman Allah ki barni na tafi karsu cinye abincin nan su hana ni idan banci ba wlh zazzabi zai iya kamani, har mafarkin shinkafar nayi, wai gani inata zubawa baƙi” faɗa tare da birgima kan ta barmar, ganin da tayi Fatu zata tara mata jama’a ne ya sata cewa “toh naji tashi ki tafi saura kuma kije ki ɗebo min fad’a ki dawo”.
tashi tayi tana washe haƙura tace “na gode sosai Inna insha Allah ba wanda zanyi faɗa dashi, kuma idan nayi Aure nai ciki wallahi ke zan bawa ɗan halak malak”
ta faɗa tare da sa wani takalminta yar ruba ruba blue color ta ruga a guje tabar gidan.
Girgiza kai Inna tayi tace “Allah ya shiryeki Fatu”…
T