*In the name of Allah the most gracious the most merciful*
🅿️01
Zara-zaran yatsun hannunta wanda suke sanye da zobina masu matukar kyan gaske da d’aukar hankali ,idona ya soma hangowa sanadiyyar motsa hannun da take tana juya stearing tana ɗan kad’asu lokaci-lokaci saboda wak’ar dake tashi a cikin Motar, tare da fitar sautin siriryar muryarta me dadin saurara.
‘I don’t care who you are, where you from what you did as long as you love me’. sautin dake tashi kenan a cikin motar na Back Street Boys wanda take marming kamar ita tayi shi.
yayinda a hankali take motsa lips dinta kamar batason motsasu, gefe guda kuma zuciyarta ke bugawa da matsanancin karfin gaske wanda ta rasa dalili faruwar haka tun safe ta tsinci kanta cikin tsanani faduwar gaba ..
Shiru motar baka jin sautin komai sai na qarar sautin wakar dake tashi a hankali ta ɗauki hanyar TANWER HOSPITAL dake Ikeja in side …
Kyakkyawar yarinya ce ajikin farko siririya mara kiba mai kyakkyawar fuska dake ɗauke da siririn hancin Kamar an zana mata shi ,mai dara daran idanu dake zagaye da gashin ido da gira , ba’a iya ganin kwayar idannunta saboda Black sunglass dake sanye a face dinta ita ba fara bace haka Kuma ba za’a kirata da baka ba chocolate colour ce me kyan gaske kamar ita tayi kanta dan rashin kibarta qara mata kyau yayi adalilin dukiyar fulaninta dake cike bam da qirjinta ,yanayin fatar jikinta kawai zaka kalla kasan daga irin gidan data fito dan asalin kamala ta ya’yan masu arziki sun zauna mata ajiki babu karya ,kayan jikinta kuwa tun daga kan rigar jikinta takalminta handbag har zuwa kan agogon dake d’aure a tsintsiyar hannunta tsadaddun gaske ne ..
Lokaci guda sautin Motar ya sauya ‘Cardi! Cardi!……wooo Leave a bitch alone….’ da sauri ta dannah receive batare data kallah wanda ke calling d’in nata ba.
“Tan Baby”. Da sauri jin me kiran nata yasa ta kalla inda wayar ke ajiye tare da yatsina fuskarta sannan ta kai hannu ta ɗauki bluetooth ta manna a kunneta ta cigaba da tuki batare da tayi magana ba .
“Kina ina? “Ya tambaya cikin low voice kamar yana ganinta.
Tabe ‘yan kananun lips d’inta tayi tana yatsina fuska sannan tace “Why?”. Ta tambaya cike da jin haushin tambayar daya mata tana kara tsura ma wayar ido , ya sauke ajiyar zuciya kamar yana kallonta.
Batare data ankara ba steary d’in hannunta ya kubce mata sai ji tayi Motar ta yi wani irin juyi , kasa controlling d’in steary din tayi take motar tayi kan wani matashi wanda yake shirin tsallakawa. “Move aside move aside!”. Abunda take iya nanatawa kenan tuni glasses din dake manne da idannunta ya cire batare data ankare ba.
Idannunta ya firfito waje shima ita yake kallo yana kokarin janyewa yana daga mata hannu alamun ta kauce cikin rashin sa’a saida ta dan goge shi sannan ta tafi ta bugi wani gini dake gefe.
“Innalillahi!”. Kalmar daya furta kenan yana kallonta wacce tuni kanta ya bugu da steary din tare da samun makwanci akai.
da sauri yayi kanta ya bude murfin dake gefenta. “Baiwar Allah baiwar Allah! Ya fada cikin rude’wa ganin jinin dake diga daga goshinta tana kallonshi tana lumshe ido alamun tana so ta mishi magana, amma ina tuni idannunta suka rufe ta kasa aiwatar da komai , tunda yake bai taba ganin macen data mishi kyau ba irin ta, kallonta kawai yake baya ko kifta idanunshi yana jin zallar bacin rai na ratsashi “ko tunanin me take da har take ƙoƙarin ganganci da rayuwata da tashi rayuwar ? a hankali ya ja tsaki yana furzar da iska mai zafi .
“Hello! Hello!! Hello Tan!!! Talk to me baby me yasa kikai shiru? Are you alright?”. Duk na cikin wayar ke wannan surutan kyakywan matashin dake tsugune gefenta ne yaji wadan nan tambayoyin bai bada amsa ba inda yasa hannu ya shiga kiciniyar cire seat belt din dake zagaye a jikinta dan a samu a bata taimakon gaggawa.