fbpx
Friday, September 12, 2025
25.3 C
Abuja

Kazar Kwanci By Rufaida Omar

Kazar Kwanci By Rufaida Omar

*1)*

 ” Mairamu! Mairamu!!”

Matar dake zaune saman kujera ƴar tsugunno dafe da kumatu yayinda ɗaya hannun ke riƙe da buta ta yi firgigit ta farka daga kogin tunanin da ta lula har ba ta san da wanzuwar mutum ba sai jin kiran da ta yi a can cikin kanta. Ta dube shi sai kuma ta yi saurin ajiye butar ta miƙe tana ɗan ɗingisa ƙafarta da ta yi tsami dalilin jimawar da ta yi a zaune ta miƙa hannu domin karɓar ledar da ya shigo da ita tana fadin.

“Sannu da zuwa Malam, yanzu ka ke tafe?”

Wanda ta kira da Malam cike da damuwa ya girgiza kai, madadin ya miƙa mata ledar sai ya riƙe ya soma magana a tausashe.

“Tun yaushe na shigo nake ta sallama ba ki amsamin ba, anya kuwa Mairamu rayuwa za ta tafi a haka? Ki rufamin asiri naji da damuwa ɗaya kar ki haifarmana da wata ki kwanta ciwo.”

Kanta a ƙasa ta share kwallar da ya zubo mata.

“Toh Malam. In sha Allahu zan kiyaye.”

Daga haka ta sa hannu ta karɓi ledar ta kai masa ɗaki sannan ta koma ta zubo ruwa a kwanon tasa ta ajiye mishi a saman ɗan teburin dake falonsa. Shi kuwa koda ya shigo falon kai tsaye ɗakinsa ya shiga ya faɗa banɗaki, kafin ya fito ta koma tsakar gidan ta yi alwala don tuni an soma kiraye-kirayen sallar Magriba. Shi din ma yana fitowa daga dakin ya nufi hanyar fita zuwa masallaci sai ya dakata ta hanyar juyowa ya kalle ta.

“Ki kira Hafsatu ki ce maza ta sa a maido yaran nan gida.”

Ta dube shi tamkar za ta yi magana sai kuma ta hadiye ta amsa da toh. Koda ya fita sai da ta gabatar da sallah ta ɗan yi addu’o’inta da ta saba kafin ta dauki waya ta yiwa Hafsatu flashing. Ko mintuna uku ba su cika ba ta biyo bayan kiran. Sai da suka gaisa ta ce.

“Babanku yace ki sa a kawo yaran nan gida.”

Daga can Hafsatu ta amsa.

“Inna ba za’a bari zuwa gobe ba sai na kawo su da kaina? Yanayin Hajara fa har yanzu babu sauki sai ta wuni ba ci ba sha sai aikin kuka.” Inna Mairamu ta numfasa, ta sani dole Hajara ta shiga damuwa tsantsa ta yadda zai wahala lokaci guda ace komai ya wuce a wajenta. Ace har sau hudu ana neman aurenka a fasa? Sati biyu kenan da yi amma har lokacin ba a bar gulma da kuma zunɗensu a unguwa ba. Wasu su ce asiri ne kishiyar uwarta (Inna Mairamu) ta yi mata shi ne dalilin da yasa hakan ke faruwa don ba ita ta haife ta ba. Yayinda wasu ke Allah wadai da masu halin munana zato ga Inna Mairamu da suka yiwa shaidar arziki.

“Hello, Inna kina jina?”

Sai a lokacin ta dawo hayyacinta.

“Ina jinki Hafsatu, hakanan za ta dawo gidan tunda Babanku ya yi umarnin. Zan dai roƙi alfamar ya bari zuwa goben ki taho da su.”

“Shikenan Inna, Allah ya nuna mana.”

Buy Affordable Data Here

Inna ta amsa da amin kafin su yi sallama, kaf yaran Malam a mata babu wata da ta ɗauke ta tamkar uwa irin Hafsatu. Ita ce babbar ɗiyarsa a mata idan ka cire manyan samarin yaransa su huɗu wadanda su ma a gidan ta tarar da su. Gaba daya yaran Malam su tara ne cif, biyu ne kaɗai yaranta. Hashimu, Sadik (wanda suke kira da Baba Habu), Mustafa, Zakari, Hafsatu, Safiyya da Hajara gaba ɗaya mahaifiyarsu ɗaya sannan mahaifiyarsu ta kasance yar uwar Malam, wannan yasa dangin Malam da dangin mahaifiyartasu a dunkule suke wuri guda, sai bayan rasuwarta ne Malam ya auri Inna Mairamu, dangin Malam kaɗan a cikinsu ne ke sonta, hakanan yaran Malam din, Hafsatu ce kusan tasu ta zo ɗaya sai ko Zakari ɗan baruwansa, amma sauran komai Inna Mairamu ta yi ba ta taɓa wanke kanta a wajensu.

Haka ta dinga hakurin zama har ta haifi yaranta biyu duka mata.

*PAID BOOK*

*KAZAR KWANCI*

*Free pages*

_*Haɗakar fiƙrah littattafai uku ne na marubuta👇🏽*_

Rufaida Umar

👉🏽KAZAR KWANCI.

Fareeda Abdallah

👉🏽RANAR NAKA.

Jeeddah Lawals

👉🏽NADIA

Farida Abdullahi

02

Malam ba shi da ra’ayin hana yara karatu, shi ɗinma tsohon Malamin makarantar gwamnati ne da a yanzu ya yi ritaya ya buɗa shago babba na siyar da litattafan makaranta iri-iri a kasuwar sabon gari. A yaransa mata Hafsatu da Safiyya duka koyarwa suke yi sai ko Hajara da ta fi su basira da son karatun wacce tun tana ƙanƙanuwa take da ra’ayin zama Likita.

Lokacin da mahaifiyarsu ta rasu tana aji na uku a ƙaramar sakandire.

Bayan auren Malam da Inna Mairamu kuwa, fitsara iri-iri ta ke yi mata.

A wasu lokutan Malam bai fiye tsawatarwa Hajara ba saboda a cewarsa tausayi take ba shi don ba karamin shagwabar da ita Mahaifiyarta ta yi ba sai gashinan lokaci ɗaya mutuwa ta yi mata yankan kauna. Komai take so yana kokarin yi mata, Inna Mairamu ma duk iyaka kokarin da take na kyautata mata Hajara ba ta gani, asalima komai ta yi mata sai tace ai dama dukiyar mahaifinta ne ita ba ta da kudin da za ta kyautata mata da shi tunda ba ta aikin komai kuma ko boko ba ta je ba asalima tun a can Nanny ce a makarantar da Malam ya koyar a baya kafin ya yi ritaya kuma ya zo ya aure ta. Abin yakan yiwa Inna Mairamu ciwo matuƙa amma hakanan take dannewa. Mace ce marar son hayaniya ko kadan, dama can an santa da hakuri, rasuwar mijinta na farko ne ya sanya ta zawarci da kananan shekaru saboda auren wuri aka yi mata. Ba ta taɓa haihuwa da tsohon mijinta ba sai bayan da ta auri Malam. Tashin farko ta haifi ɗiya mace, ta kuma roƙi alfamar Malam akan ya sanya sunan mahaifiyarta wacce ta ke tsananin so kuma ta rasu ta bar ta tun tana ƴar shekaru goma. Malam ya yi mata wannan karar ya sanyawa ɗiyar suna Sadiya. Ta ji dadi kwarai, wanda hakan ba ƙaramin baƙanta ran su Hajara ya yi ba don sun ci burin ace sunan mahaifiyarsu ya mayar, ta tsani Sadiya tsana ba kaɗan ba. Inna ta shanye abubuwa da yawa akan Sadiya. Sai ya kasance masu so da kaunar Sadiya a yaran Malam, Zakari ne kawai sai ko Hafsatu. Su Mustafa dama babu abin da ya yi musu zafi da Innar don sai ta dau dogon lokaci ba ta sanya su a idanu ba. Idan sun so ganin mahaifinsu, kodai su shiga dakinsa ta kofar waje, ko kuma su bishi can kasuwa. Safiyya kuwa duk radda ta zo gidan sai ta yadawa Inna baƙaƙen maganganu ita da Hajara sannan take tafiya. Sadiya tana da shekara uku a duniya, Inna ta ƙara haihuwar ɗiya mace wacce ta ci sunan mahaifiyar su Hajara, Asma’u suke kiranta da Husna.

Hot this week

Sri Lanka’s newly elected President Dissanayake vows to purify public administration.

Sri Lanka's new President Anura Kumara Sri Lanka has welcomed...

Labour and the Federal Government sign MoU on minimum wage adjustments.

The federal government's newly formed committee on consequential salary...

The Independent National Electoral Commission (INEC) will commence the collation of Edo election results in a few hours.

Edo Election The Independent National Electoral Commission (INEC) has officially...

JIBWIS DONATED 1 RICE TRAILER TO BORNO WATER FLOOD VICTIMS

JIBWIS NIGERIA The IZALA association has recently undertaken a remarkable...

BREAKING: I know there’s hardship, says Tinubu

At a meeting with the Forum of Former Presiding...

Topics

Sri Lanka’s newly elected President Dissanayake vows to purify public administration.

Sri Lanka's new President Anura Kumara Sri Lanka has welcomed...

Labour and the Federal Government sign MoU on minimum wage adjustments.

The federal government's newly formed committee on consequential salary...

The Independent National Electoral Commission (INEC) will commence the collation of Edo election results in a few hours.

Edo Election The Independent National Electoral Commission (INEC) has officially...

JIBWIS DONATED 1 RICE TRAILER TO BORNO WATER FLOOD VICTIMS

JIBWIS NIGERIA The IZALA association has recently undertaken a remarkable...

BREAKING: I know there’s hardship, says Tinubu

At a meeting with the Forum of Former Presiding...

Ogun Instructs Employees on Productivity.

Ogun Instructs Employees on Productivity. The Ogun State Commissioner for...

Oyebanji Wishes Tinubu’s Wife a happy 64th Birthday.

Oyebanji Wishes Tinubu's Wife a happy 64th Birthday. Ekiti State...

Rewane Predicts Nigeria’s Economy Will Reach $400 Billion by 2026.

Bismarck Rewane, the Managing Director and Chief Executive Officer...
spot_img

Related Articles

Popular Categories

spot_imgspot_img