(The story of the hard kingdom)
             Nah
  Marubuciyar Zamani
NABILA RABI’U ZANGO
     (Nabeelert Lady)
Season 1⚜5
       Babban mutum ne, kuma kyakkyawan dattijo wanda akalla baze wuce shekaru 50 aduniya ba, acikin keken guragu aka turoshi wanda da alama yana fama da mutuwar shanyewar barin jiki, daga dakin gashi aka fito dashi bayan angama gasa mashi jikinshi, wanda ake masa duk bayan kwana 3.
   Sarki Qaseem ne yashigo dakin wanda yakasance kanine ga dattijon dayake bisa kujera. Sannu Yaya yakarfin jikin? Kwalla ce tacika idonshi, wadda tariga da tazamar mashi sabo aduk lokacin dazeyi magana, Babban bawan dayake kusa dashi wanda yazama shine hadiminshi yasaka kyalle yayi saurin goge mashi idonshi.
Hannu Sarki Qaseem yadaga, nan take kowa yabar dakin. Zama yayi kusa dashi yadafa kafarshi, fuskarshi cike da damuwa, yace Yaya dan Allah kayi hkr, yakamata ace zuwa yanzu kayi hkr da abinda yafaru shekaru 18 dasuka wuce. Akullum semunsa manyan malamai sunyi addu,a akan damuwar datake cikin masarautar nan. Kuma kasan ba,a fidda rai da rahamar Ubangiji. Murmushi yayi tare da girgiza kai, yana kallon kaninnashi, wanda yake so sosai, kasancewar shikadai gareshi kuma Uwa daya Uba daya suke.
   Sarki Qaseem shima murmushin yayi ganin Yayanshi yanayi, yace tabbas Yaya yau naji dadin ganin murmushi afuskarka, wanda rabon dakayi hakan tunkafin karasa farincikinka. Segashi yau kayimun murmushi.
Dariya ce tafito daga cikin dakin, wanda wasu manyan mata ne, zaune acikinshi. Daya daga ciki tace, ai wlh Medaki kema kinsan bazan taba barin aci mana fuska acikin gidan sarauta ba, kamar yanda kikazo kika sameni acikin gidan nan shekarata nawa kika sani muna tare da Memartaba, kuma nayi hkrn zama dashi, harkikazo kika sameni, kekanki dabakiyi biyayya ba, ai da tuni nayankar maki Ticket nabarin duniyar baki daya.
 Dariya Medaki tayi tace haba Gimbiyar Babbar Gida, aini kinganni nan, tunda nataso haka Allah yayi ni, bandamu dasena zama babba ba, inde zanzama ‘yar kore kuma inkarbu toni banida damuwa, zan iya yinkoma menene. Dan haka kada kidamu, koda yanzu bamune matan sarki Qaseem ba, aide kanin mijin mune. Kuma aide haryanzu muna cikin masarautar.
Gimbiyar Babbar Gida tadauki apple tasa abakinta, ta maida kallonta gurin Jakadiya, wadda take mata tausa tace, Jakadiya bamu labarin cikin gida. Jakadiya ta gyara zama tace Allah yatemakeki Babbar Gimbiya, wadda babu kamarta, ba,ayi ba, kuma baza,a tabayin kamarki acikin gidan nan ba. Allah yakara tsawon kwana. Babu wani labarin daze firgitaki acikin gida, kinriga dakinsan Gimbiya Shuwa haryanzu bata yarda dani ba. Narasa dalilinta nayin haka, ace mace duk wani hali irin na mijinta Sarki Qaseem tadaukeshi. Kodan ita tata sarautar gado ce, shiyasa bata yarda da kowa? Medaki tace haba Jakadiya atunanina babu wani abu daze baki tsoro acikin masarautar nan, kinsan ketamu ce, muma haka. Dariya tayi tace hakane, Gimbiya, karku damu asannu zakusha labari.
Zaune take cikin wasu kodaddun kaya, acikin wata bukka ta kara, wadda take daga gefen wata tsohuwar MAKABARTA. Wani tsohon kwanone ahannunta,abinci ne, aciki wanda gaba dayanshi bewuce rabin kwanonba. Kyakkyawar matashiyace wadda bazata wuce shekaru 18 aduniya ba. Akusa da ita wata dattijuwa ce, wadda itama bazata wuce shekaru 38 aduniya ba, da kaganta zakasan tana cikin yanayi na hauka, gaba daya kamanninta sun bata. Jawota diyarta tayi tana mata magana irin ta kurame, tana mata nuni da kwano alamun taci abinci.